Amurka za ta aika kayan yaki Iraqi

Masu tada kayar baya a kasar Iraqi
Image caption Ana ci gaba da ba ta kashi tsakanin masu tada kayar baya da dakarun gwamnatin Iraqi.

Amurka tace za ta kara aikewa da kayan yaki zuwa kasar Iraq, domin taimakawa gwamnatin kasar a yakin da ta ke yi da kungiyoyin masu tada kayar baya da ke yammacin yankin Anbar.

Fadar White House ta ce za'a tura karin jiragen yaki mara sa matuka a makonni masu zuwa, tare da karin wasu makamai masu linzami da aka yi wa lakabi da Hellfire a turance a wata mai zuwa.

Yankin Anbar da ke yammacin Iraq dai bai taba fuskantar bata kashi irin wannan ba a shekaru da dama.

Tashin hankalin da ake yi ya tilasta wa mazauna yankin hijira domin tsira da ransu a wasu sassan kasar.

Karin bayani