Hollande na son hana mai ban dariya wasa

Image caption Dan wasan ban dariya Dieudonne ba ya goyon bayan kafa kasar Isra'ila.

Shugaban kasar Faransa, Francois Hollande ya bukaci jami'ai da su tabbatar da haramcin da aka yi wani mai labaran ban dariya mai suna Dieudonne M'bala M'bala, wanda ake zargi da kin jinin Yahudawa.

Mr Hollande ya umarci jami'an Faransa da su hana Dieudonne gabatar da wasansa saboda abin da ya kira gudun tada zaune tsaye.

Magadan garin biranen Faransa da dama dai sun soke wasan da Dieudonne ya shirya yi a wannan makon a fadin kasar.

Sai dai Dieudonne ya ce zai daukaka kara bisa dogaro da dokar 'yancin fadin albarkacin baki ta Faransa.

Sau shida dai ana samun Dieudonne da laifin cin zarafin Yahudawa a baya.

Karin bayani