Mayakan ISIS sun kashe mutane 50 a Syria

Image caption Dakarun ISIS masu kishin Islama na yaki da Musulmi masu sassauci a Aleppo, Syria.

Masu fafutuka a birnin Aleppo da ke arewacin Syria sun ce 'yan bindiga masu alaka da al-Qaeda sun kashe mutane 50 daga cikin wadanda suka kama.

Sun ce wadanda aka kashe sun hada da likitoci, 'yan jarida da kuma mayakan wasu kungiyoyin 'yan tawayen da suke adawa da su.

Sai dai babu wata hukuma mai zaman kanta da ta tabbatar da rahoton kisan.

Mayakan kungiyar ISIS mai alaka da al-Qaeda na yaki da kungiyoyin Musulmi masu sassaucin ra'ayi a Aleppo.

Karin bayani