Mahara sun kashe mutane hudu a Kaduna

Image caption 'Yan sandan Nigeria na fama da 'yan bindiga da mahara.

Wasu mahara a jihar Kaduna da ke arewacin Nigeria sun kashe 'yan sanda uku da farar hula guda a cikin motar daukar kudi ta banki.

Maharan da ke kan babura sun bude wa motar kudin wuta ne inda suka hallaka 'yan sandan da kuma direban motar.

Shaidu sun ce maharan sun yi awon gaba da makudan kudi bayan kashe mutanen.

Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar Kaduna, DSP Aminu Lawal ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai ya ce kawo yanzu babu tabbas ko 'yan fashi ne ko kuma 'yan bindiga.

Karin bayani