'Yan bindiga sun kai hari a Pilato

Image caption An kai hari a kauyen karamar Hukumar Riyom

Rahotanni daga jiharPilato da ke arewa ta tsakiyar Nigeria na cewa wasu 'yan bindiga da kawo yanzu ba'a iya tantance ko su wane ne ba sun kai hari karamar hukumar Riyom inda aka samu asarar rayuka; wasu kuma suka jikkata.

Kawo yanzu dai ba'a iya tantance adadin mutanen da suka rasa rayukansu ba, yayin da mutane fiye da 10 su ka samu munanan raunuka.

'Yan bindigar sun budewa mazauna wani kauye wuta tare da kona gidaje.

Lamarin dai ya faru ne a kauyen Shonong da ke jihar Pilato, inda ake yawan samun tashe-tashen hankula wanda yawanci rikicin tsakanin Musulmai ne da mabiya addinin Kirista saboda filaye.

Karin bayani