Daliban Nijar na kauracewa ajujuwansu

Image caption Daliban sakandire na neman a kyautata ilimi a Nijar.

Daliban makarantun sakandire a Yamai, babban birnin jamhuriyar Nijar na kaurace wa ajujuwansu tsawon kwanaki biyu.

Daliban na neman tilasta wa hukumomin ilmi ne su shawo kan matsalolin da suka ce na kawo koma baya ga tafiyar ilmi a jihar.

Matsalolin sun hada da rashin wadatar malaman makaranta, teburan karatu da kuma kakkafa ajujuwan zana da suka yi kadan.

Sai dai hukumomin ilmin na cewa kusan duk kan matsalolin da daliban suka gabatar an kusa shawo kansu.

Karin bayani