Mutane 16 sun mutu a harin Pilato

Image caption Dubunnan mutane sun mutu a rikicin Pilato a shekarun baya.

Rundunar tsaro ta musamman mai aikin kiyaye zaman lafiya a jihar Pilato ta Nijeriya ta tabbatar da mutuwar mutane 16 a harin da aka kai ranar Litinin a kauyen Shonong a karamar hukumar Riyom, yayin da aka jikkata wasu da dama.

Maharan da aka ce masu yawan gaske ne, sun yi amfani da bindigogi da adduna ne kana sun kona gidaje da dama.

Mazaunan yankin dai sun ce mutanen da aka kashe sun kai 30, abin da rundunar tsaron ta musanta.

Rundunar tsaron ta ce ta na kokarin farauto maharan don gurfanar da su gaban shari'a.

'Yan-kabilar Berom da Rundunar tsaron na zargin Fulani makiyaya ne da kai harin, sai dai Fulanin suna ce neman bata masu suna kawai ake yi.

Jihar Pilato ta dade tana fama da rigingimu masu nasaba da kabilanci da addini da kuma siyasa inda matsalar ta fi kamari tsakanin kabilun Berom da Fulani wadanda sau da yawa kan zargi junansu da kai hari ko kuma satar shanu.

Karin bayani