Rikicin jihar Delta ya tarwatsa al'umma

Image caption Gwamnan Delta Emmanuel Uduaghan ya musanta faruwar rikcin kodayake 'yan sanda sun tabbatar.

Mazauna garin Ugborodo a jihar Delta dake kudancin Nigeria na kauracewa garinsu bayan da fada ya barke tsakanin bangarorin al'umma biyu.

Shaidu sun ce matasa kimanin 400 ne suka kone gidaje tare da yin harbe-harbe a bindiga sanadiyyar takaddama kan kafa cibiyar fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje da gwamnatin jihar za ta kafa a garin.

Yayin da wani bangare ke na'am da shirin, daya bangaren ya ki amince wa saboda a cewar su ba'a yi yarjejeniya da jama'ar garin game da diyyar da za'a biya su ba.

Rundunar 'yan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin kodayake gwamnatin jihar Delta ta musanta afkuwarsa, inda ta ce makiyan ci gaban jihar ne ke yayata jita-jitar afkuwar rikicin.

Karin bayani