'Mutane 34 ne aka kashe a harin Shonong'

Wata 'yar sanda a Najeriya
Image caption Wata 'yar sanda a Najeriya

Gwamnatin jihar Filato a Nijeriya ta bayyana cewa mutane talatin da hudu ne aka tabbatar da mutuwarsu kawo yanzu a harin da wasu 'yan bijdiga suka kai jiya a kauyen Shonong dake karamar hukumar Riyom.

Kwamishin yada labarai na jihar , Mista Yiljap Abraham shi ne ya bayyana hakan a wata hira da BBC.

Harin dai ya yi sanadiyyar tarwatsa mutane kimanin dari shida suka rasa matsugunansu su koma wurare daban-daban a yankin.

Hakanan kuma an kona dimbin gidaje da rumbunan hatsi.

Alkaluman gwamnatin dai sun saba da wadanda rundunar tsaro ta musamman mai kiyaye zaman lafiya a jihar ta Filato ta bayar, wadanda ke nuna cewa mutane goma sha shida ne suka rasa rayukansu a harin.

Kawo yanzu dai wadanda suka jikkata suna ci gaba da karbar magani a asibitoci a Jos babban birnin jihar.

Karin bayani