Goodluck Jonathan na tare da Sambo

Shugaba Jonathan da mataimakinsa Namadi Sambo
Image caption Ana zargin dai 'yan adawa ne ke son haddasa rikici tsakanin shugaban Najeriyar da mataimakinsa.

Fadar shugaban kasar Nigeria ta ce babu mai raba su da mataimakinsa, Architect Namadi Sambo muddin shugaba Jonathan zai tsaya takara badi.

Bangaren shugaban kasar dai na bayyana matsayinsa ne sakamakon wasu maganganun da ake yi na yiwuwar raba-gari da mataimakin nasa.

Hakan ya biyo bayan sauya-shekar da wasu magoya bayan jam'iyyar PDP mai mulki suka yi a jihar Kaduna, jihar da mataimakin shugaban kasar ya fito, lamarin da wasu ke cewa alama ce ta raguwar tagomashinsa a tsakanin magoya bayansa.

Mai bai wa shugaban Nigeria shawara a kan harkokin siyasa, Ahmed Gulak ya yi zargin cewa abokan adawa ne ke neman bata tsakanin shugaban kasar da mataikin nasa.