Turkey ta kori 'yan sanda 350

Image caption Gwamnatin Turkey na zargin 'yan sanda da kulla ma ta manakisa.

Gwamnatin Turkey ta kawar da jami'an 'yan sanda 350 daga mukamansu a Ankara, babban birnin kasar sanadiyyar binciken cin hanci da rashawa da su ke yi wa makusantan gwamnatin.

An sallami daruruwan 'yan sanda daga aiki tare da sauya wa wasu wurin aiki tun bayan fara binciken a watan jiya.

Ministoci uku kuma sun ajiye mukamansu bayan da ake tsare 'ya'yansu a binciken.

Pirai ministan Turkey ya zargi 'yan sanda da hukumomin shari'a da kulla wata manakisa don bata sunan gwamnatinsa.

Karin bayani