An kwatanta shugaban Zambia da dankali

Image caption An danganta shugaban Zambia Michael Sata da dankali saboda rashin jin shawara.

An tuhumi wani dan adawa a Zambia da bata sunan shugaban kasar bayan da ya kwatanta shi da dankali.

Frank Bwalya ya kwatanta shugaba Michael Sata ne da dankali ne wanda ke karye wa idan aka tankwara shi.

A na amfani da wannan karin maganar ne a harshen Bemba domin misalta mutumin da ba ya jin shawara.

Idan har kotu ta samu Mr Bwalya da laifi zai iya fuskantar hukuncin daurin shekaru biyar a gidan yari.

A shekarar 2002 ma an kama editan wata jarida a kasar saboda ya kwatanta shugaban kasar wancan lokaci, Levy Mwanawasa da kabeji.