An kashe mutane 26 a Lubumbashi

Image caption Dakarun gwamnatin Congo sun kori 'yan tawayen

Akalla mutane 26 aka kashe a fafatawar sa'o'i takwas tsakanin dakarun gwamnati da 'yan tawaye Lubumbashi, gari na biyu mafi girma a jamhuriyar dimokradiyyar Congo.

'Yan sanda sun ce an fatattaki 'yan tawayen da safiyar Talata bayan da aka kwana ana gumurzu.

Sun kuma ce mutane sun watse daga birnin mai mazauna fiye da miliyan guda.

'Yan tawayen Mai Mai Kata Katanga, masu ne su ka kai farmaki birnin.

Kungiyar dai na fafutukar neman 'yancin yankin Katanga ne, wanda shi ya fi arzikin ma'adinai a jamhuriyar dimokradiyyar Congo.

Karin bayani