Tsamin dangataka tsakanin India da Amurka

Image caption India da Amurka abokai ne na kut-da-kut

Dangantaka tsakanin India da Amurka na kara tsami bayan rashin jituwar da suka samu saboda tsare wata jami'ar diplomasiyyar India da aka yi a New York a watan Disamba.

India ta bukaci Amurka da ta janye iznin shiga wani wurin shakatawa a Delhi ga duk Amurkawan da ba jami'an diplomasiyya bane.

Ta kuma ce yanzu doka za ta yi aiki a kan duk wata mota mai lambar ofishin jakadancin Amurka da ta keta dokokin hanya a kasar.

A watan Disambar bara ne aka tsare wata jami'ar diplomasiyyar India a Amurka, a bisa zargin biyan wata ma'aikaciyar ta kudi kasa da yadda ta ce za ta biya a takardun da ta cike na neman iznin shiga kasar, zargin da ta musanta.

Karin bayani