An dage shari'ar Mohammed Morsi

Image caption Magoya bayan Mohammed Morsi

Kotu a Masar ta dage sauraron shari'ar da ake yi wa hambararren shugaban Masar, Muhammed Morsi, har sai farkon watan Fabarairu.

Alkalin ya ce rashin kyawun yanayi ya hana helkoptan da zai kawo Mista Morsi daga Iskandiriya taso wa zuwa birnin Alkahira.

Sai dai daya daga cikin mutumin da ake tuhumarsa da Morsi din wato Essam El-Erain ya yi magana da karfi a cikin kotun inda yace Morsi ba zai hallarci zaman kotun da yake haramtacce ba.

Ana zargin Morsi da wasu manyan jami'an gwamnati da janyo kashe masu zanga-zanga a shekara ta 2012 kafin sojojin suyi masa juyin mulki.

Ana kuma tuhumarsa da hada baki da mayakan sa-kai na kasashen ketare wajen balle kurkuku.

Karin bayani