Ma'aikatan mai sun fasa yaji a Nigeria

Image caption NUPENG da PENGASSAN sun janye shirin tafiya yajin aiki

Kungiyoyin Ma'aikatan man fetur a Nigeria, NUPENG da PENGASSAN sun janye barazanar da suka yi ta fara yajin aiki.

Kungiyoyin sun yi shirin tafiya yajin aikin ne ranar Laraba sakamakon shirin da gwamnati ke yi na sayar da matatun man fetur na kasar.

Kungiyoyin sun yanke shawarar ne cikin daren Talata bayan kwashe tsawon lokaci suna tafka muhawara kan batun da ministocin kwadago da man fetur na Najeriyar.

A karshen taron dai gwamnati ta bayyana cewar ta janye shawarar sayar da matatun man.

Karin bayani