Stella Oduah ta ki ta ce kome kan zargin takardun boge

Image caption Gimbiya Stella Oduah

A Najeriya mukarraban Ministar sufurin jiragen sama ta Najeriya, Ms Stella Oduah, sun ce ba za su mayar da martani ba dangane da wani zargi da ya janyo wani sabon cece-kuce game da Ministar.

Mr Yakubu Datti, jami'in hulda da jama'a na hukumomin sufurin jiragen sama na Najeriya, ya ce sun yanke shawara cewa ba za su ce uffan ba game da zargin rashin sahihancin shaidar takardar kamalla karatun digiri na biyu da ake yiwa ministar sufurin jiragen saman kasar, Stella Oduah.

Kafar watsa labarai mai kwarmata bayanai Sahara Reporter ce ta soma tsegunta cewar ministar ta ce tana da takardar babban digiri daga wata makaranta a Amurka, amma kuma da kafar ta tuntubi makarantar sai mahukunta kwalejin suka ce basa bada shaidar takardar digiri na biyu wato masters a fannin da ministar tayi ikirarrin tana dashi.

Yanzu haka dai labarin da ya yadu kamar wutar daji a shafukan zumunta na zamani irinsu Twitter da Facebook a Nigeria.

Ita dai Minista Stella Oduah ta saba fuskantar cece-kuce, saboda dai itace wacce aka samu da laifin sabar ka'idar siyan wasu motoci masu sulke wadanda harsashi bai hudasu a kan kusan naira miliyan 250, abinda ya janyo tada jijiyoyin wuya a kasar gannin irin dinbin jama'ar dake kwana cikin wunya da kuma miliyoyin yaran da ba sa zuwa makaranta duk da dinbim arzikin kasar.

Karin bayani