Mashaya sigari sun kusa biliyan

Image caption Nigeria na kan gaba a karancin busa sigari.

Adadin masu shan sigari a duniya ya kusa kai wa biliyan daya, a cewar wani sabon bincike.

A 2012, mutane miliyan 967 ne ke shan sigari kullum sabanin miliyan 721 a shekarar 1980, kamar yadda alkalumma daga kasashe 187 su ka bayyana.

Masu bincike a jami'ar Washington ta Amurka sun ce kodayake masu shan tabar na karuwa, kasonsu cikin adadin al'ummar duniya baki daya raguwa yake.

Kimanin kaso 31% na maza a fadin duniya na busa sigari yayin da kaso 6% na mata kan busa a yanzu sabanin maza kaso 41% da mata kaso 10% a 1980.

Nigeria na kasa

Kididdigar ta nuna cewa fiye da rabin mazajen Rasha da Indonesia na shan taba a kullum.

Kasar da aka fi shan taba ita ce East Timor inda kaso 61% ke zuka yayin da kasashen Antigua da Barbuda ne su ka fi karancin shan taba da kaso 5%.

Nigeria ce ta uku a jerin kasashe masu karancin mashaya taba sigari.

Kasashe irin su Canada, Iceland, Norway da Mexico ne suka fi kowanne nasarar rage adadin mashaya sigari.

Da sauran aiki

Jagoran masu binciken Dr Christopher Murray, ya ce duk da nasarar da aka samu kan rage shan taba, akwai sauran gagarumin aiki a gaba.

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce za'a iya ceton rayuka da dama ta hanyar tsaurara matakan hana zukar sigari ta hanyar kara haraji, gargadi akan kwalin tabar da kuma hana busa sigari a wuraren taruwar jama'a.

A fadin duniya kaf, mutane sun zuki karan taba sigari tiriliyan 6.25 a shekarar 2012 idan aka kwatanta da kara tiriliyan 4.96 a shekarar 1980.