'Yan majalisar Sokoto sun koma APC

Image caption Gwamnan Sokoto Aliyu Wamakko na cikin gwamnonin da su ka bar PDP zuwa APC.

'Yan majalisar dokokin jihar Sokoto da ke arewacin Nigeria 27 daga cikin 30 sun sauya sheka daga jam'iyyar PDP mai mulkin kasar zuwa jam'iyyar adawa ta APC.

'Yan majalisar sun sanar da hakan ne a zaman su na ranar Laraba.

Sun kuma ce sun dauki wannan matakin ne domin amsa kiraye-kirayen da al'ummominsu ke musu na su bi bayan gwamnan jihar Aliyu Magatakarda Wamakko, wanda ya sauya sheka daga PDP zuwa APC tare da wasu gwamnoni hudu.

Rahotanni sun ce da alamun saurarn 'yan majalisar ma za su sauya shekar kasancewar ba su sami halartar zaman majalisar ba ne sanadiyyar rashin lafiya.

Karin bayani