Ana tuhumar Jami'an Amurka da zamba

Image caption Jami'an 'yan sanda da na kashe gobara sun yi rawar gani ranar harin 11/09/01 a New York.

Ana tuhumar wasu tsofaffin jami'an 'yan sanda da na kashe gobara a Amurka su 80 da suka ce sun shiga halin dimuwa ko tabin hankali sakamakon daukin da suka kai wa al'umma a lokacin harin 11 ga Satumban 2001.

Ana dai tuhumarsu da laifin yin zamba don karbar kudaden tallafin gwamnati, bayan sun yi ikirarin karya cewa sun samu tabin hankali sanadiyyar dimuwar da suka shiga a lokacin harin.

Daya daga cikin tsofaffin jami'an ya shaidawa likitoci cewa wani tsananin tsoro da yake ji na hana shi fita daga gidansa, sai kuma aka gan shi ya wallafa hotuna a shafinsa na sada zumunta a intanet da ke nuna shi yana hawa wani jirgin zamiyar kankara domin nishadi.

Ana tuhumar wasu mutane hudu da shirya zambar da kuma koyar da tsofaffin jami'an yadda za su tuburewa likitoci su nuna cewa su na da tabin hankali.

An dai tuhumi mutane 100 ya zuwa yanzu, bisa zargin tafka zanbar da ta kai $400 miliyan.

Karin bayani