Yara sun fada bala'i a CAR- UNICEF

Mayakan Seleka a birnin Bangui, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya
Image caption Mayakan Seleka a birnin Bangui, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

Asusun yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya ce rikicin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ya haifar da tururuwar mutane a sansanoni da ke birnin Bangui

Wani wakilin musamman na Majalisar Dinkin Duniya kan kare hakkin bil'adama mai lura da wadanda suka rasa matsugunansu Chaloka Beyani ya ce ana bukatar $250,000 miliyan don samar da abinci, ruwa da kiwon lafiya a sansanonin.

Asusun na UNICEF ya yi kashedin cewa Jamhuriyyar Africa ta tsakiya, wacce yaki ya daidaita na gab da fadawa wani bala'ain da ya shafi jama'a.

Wakilin Asusun a kasar, Souleymane Diabate ya ce sansanonin jama'a da suka cika suka batse da rashin tsaftaccen ruwa da muhalli sun jefa yara cikin wani bala'i.

Asusun ya ce an samu barkewar cutar kyanda a sansanin dake filin jirgin saman dake Bangui, inda yanzu haka fiye da mutane 100,000 ke neman mafaka daga fadan da ake tsakanin kungiyoyi biyu masu rike da makamai.

A ranar Alhamis ne shuggbananin kasashen Afirka za su tattauna kan rikicin dake faruwa a Jamhuriyar Afirka ta tsakiyar