China ta ci tarar N200m saboda haihuwa

Image caption Zhang Yimou zai biya N200m tarar haihuwar 'ya'ya uku.

China ta ci tarar daya daga cikin fitattun daraktocin finafinanta fiye da Naira miliyan 200 saboda haifar 'ya'ya uku, abin da ya saba wa dokar kasar da ta takaita mazaunan birane ga haihuwa daya tak.

A cikin watan Maris ne gwamnatin birnin Wuxi dake gabashin kasar ta shaida wa Zhang Yimou ce wa za'a ci tararsa.

A watan Disamba ya nemi gafara bayan ya amince da cewa haihuwar 'ya'yan uku "mummunar dabi'a ce."

Zhang Yimou ne daraktan bikin bude wasannin Olympics da aka yi a Beijing a 2008.

A Nuwamban da ya wuce ne dai China ta sassauta dokar hana haihuwa fiye da daya, inda ta bai wa mutanen da su kadai iyayensu su ka haifa damar haihuwar 'ya'ya biyu.

Karin bayani