Ghana za ta tura sojoji zuwa Sudan ta Kudu

Image caption Shugaba John Dramani Mahama na Ghana

Ghana za ta tura dakarunta 850 zuwa Sudan ta Kudu don aikin wanzar da zaman lafiya a cikin kasar da a yanzu take fama da rikicin kabilanci.

Hukumomin tsaron Ghana wadanda su ka tabbatar da haka, sun ce za a tura tawagar farko da ta kunshi dakarun 350 wadanda a yanzu haka su ke ayyukan kiyayen zaman lafiya a kasar Ivory Coast.

Tun a cikin watan Disambar bara ne aka soma tashin hankali a kasar Sudan ta Kudu tsakanin 'yan tawaye dake goyon bayan tsohon mataimakin shugaban kasar, Riek Machar da kuma sojojin gwamnati dake biyayya ga shugaba Salva Kiir.

Sakamakon rikicin dai, a yanzu haka dubban mutane sun guje daga muhallansu inda su ke neman mafaka a sansanonin majalisar dinkin duniya.

Tashin hankalin ya janyo mutuwar daruruwan mutane a Sudan ta Kudun.

Karin bayani