Za'a lalata makaman Syria a Jamus

Image caption Za'a kwance makaman Syria a jirgin ruwa kafin kone gubar a Jamus.

Jamus ta ce za ta shiga jerin kasashen duniya da ke bada gudunmawa wurin lalata makamai masu guba mallakar Syria.

Ministan hulda da kasashen waje, Frank-Walter Steinmeier, ya ce Jamus ba za ta ki sauke nauyin da Majalisar Dinkin Duniya ta dora mata ba.

Steinmeier ya ce za'a yi amfani da wata cibiyar Jamus domin kone gubar da za ta rage bayan lalata makaman a cikin wani jirgin ruwa a teku.

Shugaba Assad na Syria ya amince da mika makamansa masu guba a bara bayan da daruruwan mutane suka hallaka a wani harin iska mai guba a bayan garin Damascus.

Karin bayani