Jonathan ya bukaci Sanusi ya yi murabus

Image caption Shugaba Goodluck Jonathan da Sanusi Lamido Sanusi

Shugaban Nigeria, Dr Goodluck Ebele Jonathan ya bukaci Gwamnan babban bankin kasar, Malam Sanusi Lamido Sanusi da ya yi murabus daga kan mukaminsa nan take.

Rahotanni sun ce gwamnan babban bankin ya shaidawa Shugaban kasar ba zai yi murabus ba.

Wata majiya ta shaidawa BBC cewar hakan ya faru ne a yayin da shugaban kasar ya kira gwamnan babban bankin Najeriyar ta wayar tarho.

Shugaban Najeriyar ya zargi gwamnan babban bankin ne da kwarmata wasikar da ya rubuta, inda ya yi ikirarin cewar kamfanin NNPC bai bayyana yadda ya yi da $49.8 biliyan ta kudaden danyen mai ba.

Bayan wani zama da aka yi tsakanin kamfanin Mai na Nigeria wato NNPC da Ministar Kudi ta Nigeria, Ngonzi Okonjo Iweala da kuma babban bankin Najeriyar da Sanusi Lamido Sanusi an cimma matsayar cewa kudaden da suka rage da ba'a fayyace yadda aka yi da su ba sun dawo $10.8 biliyan.

To sai dai wata majiya ta ce mai yiwuwa duk da wannan matsaya da aka cimma kudaden da ba'a fayyace ba sun zarta hakan.