'Za a gano maharan Kwankwaso'

Gwamnan Kano Rabi'u Musa Kwankwaso
Image caption Mahaifin Gwamnan Kano ya tsallake rijiya da baya a harin da aka kai masa

Gwamnatin jihar Kano a arewacin Nijeria ta ce ta tabbatar nan bada jimawa ba, za'a gano wadanda suka kashe mutane uku a masallacin kauyen Kwankwaso ranar Talata da daddare.

A karon farko tun bayan harin, Gwamnan jihar wanda kuma mahaifinsa ya tsallake rijiya da baya a harin, ya ce harin yana kama da irin hare-haren da ake kai wa a wasu sassan arewacin kasar.

Kawo yanzu dai, babu wanda ya dauki alhakin kai harin, wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane uku da jikkata wasu fiye da 10, sai dai 'yan sanda sun ce su na bincike.

Matsalar tsaro a arewacin Najeriya ta kasance babban kalubale ga mahukunta.