Yaki da jima'i-don-kifi a Kenya

Image caption Zawarawan da aka bari da 'ya'ya ne aka fi yin jima'i da su kafin a sayar musu da kifi.

Mata a kasar Kenya na kokarin kawo karshen wata al'ada da mata masu sayar da kifin kan yi jima'i kyauta da masunta kafin su amince su rika kawo musu kifin da za su sara.

Ana dai zargin wannan al'adar da mutanen kasar ke kira "jaboya" ta taimaka wurin yaduwar kwayar cutar HIV mai karya garkuwar jiki a lardin Lake Victoria da ke yammacin Kenya.

Wata kungiyar ci gaban al'umma, VIREDI, ta kaddamar da shirin bai wa mata bashin kwale-kwalen da za su rinka yin su da kansu sannan su biya kudin a hankali.

Jami'in kungiyar, Dan Abuto ya ce za'a yi amfani da kudaden da matan ke biyan bashin ne wurin samar da karin kwale-kwalen ga wasu matan mabukata.

Ya kuma ce manufar shirin shi ne tunkarar "jaboya" a matsayin barazana ga lafiyar al'umma tare da kokarin rage talauci, da nuna bambancin jinsi.

Mafi yawa dai matan da ake jima'in da su domin ba su damar sayen kifin, zawarawa ne musamman wadanda mazansu su ka mutu su ka bar musu yara.