Nigeria da Birtaniya sun kulla yarjejeniya

  • 9 Janairu 2014
Ministan Shari'ar Birtaniya Jeremy Wright da na Nigeria Bello Adoke

Gwamnatin Najeriya da ta Birtaniya sun sanya hannu a kan yarjejeniyar musayar fursunoni.

Yarjejeniya za ta bada damar 'yan Najeriya da suka aikata laifi a Birtaniya su yi zaman kaso a Najeriya, kuma 'yan Birtaniya da suka aikata laifi a Najeriya a maida su Birtaniya su yi zaman gidan kaso.

A ranar Alhamis ne ministan shari'a na Najeriya, Bello Adoke da kuma Jeremy Wright minista a ma'aikatar shari'a ta Birtaniya su ka sanya hannu a kan yarjejeniyar a Abuja, a madadin gwamnatocin kasashen biyu.

Wani kwamiti na musamman ne dai zai sa ido a kan yadda za a aiwatar da yarjejeniyar, kuma yarjejeniyar za ta soma aiki ne kafin karshen shekara ta 2014.

Alkaluma na baya bayan nan dai na nuna cewa, akwai 'yan Najeriya fiye da 500 a gidajen yarin Birtaniya.