An kashe wani babban dan sanda a Pakistan

Kisan Aslam Chaudry
Image caption Harin da ya kashe Aslam Chaudry

Wani babban jami'in 'yan sanda, ya hallaka a wani harin kunar bakin wake da 'yan Taliban suka kai a Karachi, birni mafi girma a Pakistan.

Marigayin Chaudry Aslam, ya yi fice ne wajen yaki da 'yan Taliban, kuma a baya ya sha tsallake rijiya da baya. Akalla wasu karin jami'ai 'yan sanda biyu sun mutu a harin.

Wani jami'in 'yan sanda, Raja Umar Khittab, ya ce harin ya yi kama da irin na kunar bakin wake.

Reshen 'yan Tabilan dake Pakistan dai, sun ce su suka kai harin.

Ana daukan Chaudry Aslam dai a matsayin daya daga cikin jami'an 'yan sanda marasa tsoro a kasar ta Pakistan.

'Yan sa'o'i kafin a kashe shi, ya bayyana cewa jami'ansa sun kashe 'yan Taliban uku.