Dakarun Salva Kiir na tunkarar Bentiu

Sudan ta Kudu
Image caption Sudan ta Kudu

Dakarun da ke goyon bayan gwamnatin shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir sun nausa arewa inda su ka doshi garin Bentiu da ke hannun 'yan tawaye a yankin da ke da arzikin man fetur.

Wakilin BBC da ke Bentiu ya ce ana jin dakarun gwamnatin sun kusa isa garin, abin da ke razana farar hula.

Dubunnan mutane dai na tserewa inda da yawansu suka cunkushe farfajiyar ofishin Majalisar Dinkin Duniya.

'Yan tawayen, masu goyon bayan tsohon mataimakin shugaban kasa Riek Machar sun fara janyewa tare da lalata makaman da ba za su iya dauka ba.

Dubban mutane ne suka yi maci a Juba babban birnin kasar don nuna rashin amincewar su da yakin, da kuma a kawo karshen gwabzawar da ake yi tsakanin dakarun bangarorin biyu.

Fadan Sudan ta Kudun ya rincabe ne a watan da ya gabata, kuma ba a samu wani ci gaban a zo a gani ba game da batun tattaunawa kan kawo karshen sa.