Areva: Kungiyoyin farar hula na shirin zanga zanga

Image caption Kungiyoyin sun ce ba zasu ci gaba da jira ba

A jamhuriyar Nijar wani kawance daya kunshi kungiyoyin farar hula sama da 20 ya ce zai shirya wata sabuwar zanga zanga a ranar 25 ga wannan watan, a wani mataki na ci gaba da matsawa gwamnati da kamfanin Areva lamba.

Kawancen ya ce yana bukatar har sai bangarorin biyu sun yi wa 'yan kasar ta Nijar bayani game da inda aka kwana a cikin tattaunawar da suke yi don kulla sabuwar yarjejeniya.

Kungiyoyin farar hular dai sun ce suna bukatar bangarorin biyu su fito su bada haske ne game da sabuwar yarjejeniyar da aka kulla tare da abinda ta kunsa.

Kungiyoyin sun bayyana hakanne a cikin wata sanarwa da suka fitar a birnin Yamai.

Karin bayani