Majlaisar mulkin CAR na gana wa a Chad

Image caption Rikicin CAR yafi shafar mata da kananan yara

Daukacin wakilan majalisar mulkin rikon kwaryar Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya (CAR) sun isa kasar Chad inda shugabannin Afrika ke tattaunawa kan shawo rikicin kasar.

An dai dage taron shugabannin kasashen tsakiyar Afrika ne da talatainin daren Juma'a.

Sai dai an bukaci tawagar ta CAR su tattauna tsakaninsu game da makomar shugaban rikon kwarya, Michel Djotodia.

Ana dai matsa ma sa ne ya sauka daga mulki bayan da ya gaza kawo karshen rikicin da ake tsakanin Kirista da Musulmi, sai dai kakakinsa ya ce ba zai sauka ba.

Karin bayani