China ta dara Amurka fitar da kaya

Image caption China ta yi wa Amurka zarra a kasuwanci.

China ta ce farashin kayan da ta fitar kasashen waje a shekara guda ya zarta dala tiriliyon hudu a karo na farko, abin da ya tabbatar da matsayinta na kasar da tafi kowacce kasuwanci a duniya.

Amurka ba ta baiyana alkaluman cinikinta ba tukuna amma dai kididdigar watanni 11 ba ta wuce dala tiriliyan uku da rabi ba.

Koda yake akan yi shakku game da ingancin kididdigar cinikin China, masana sun ce ko bayan daidaita kura-kuran da akan samu, China ta zarta Amurka a fagen ciniki a duniya.