Japan za ta tallafa wa kasashen Afrika

Image caption Mr Shinzo Abe

Ana sa ran Pirai ministan Japan, Shinzo Abe zai sanar da bada tallafin fiye da dala biliyan 14 ga kasashen Afrika uku.

A ziyararsa ta mako guda a nahiyar, Pirai ministan kuma zai sanya hannu a wasu yarjejeniyoyi kan cinikayya da kuma makamashi.

Mr Abe zai ziyarci kasashen Ethiopia da Ivory Coast da kuma Mozambique.

Ana kallon ziyarar ta sa a matsayin wata hanyar kokarin gogayya da China wacce a yanzu ta zuba dubban miliyoyi a cikin nahiyar Afrika.

A Ethiopia, Mr Abe zai sanar da shirin gina wata tashar samar da lantarki.

A Mozambique kuma Japan za ta nemi zuba jari a bangaren iskar gas da makamashin kwal.

Karin bayani