Za'a habaka Arewa maso gabashin Nigeria

Image caption Rikicin Boko Haram ya karya Arewa maso gabashin Nigeria.

Gwamnatin Nijeriya ta sanar da shirye-shiryen farfado da tattalin arzikin arewa maso gabashin kasar da rikicin Boko Haram ya karya.

Za'a fara aiwatar da shirin ne a jihohin Adamawa da Borno da Yobe wadanda rikicin kungiyar nan ta Boko Haram ya fi yi wa illa, wanda a dalilinsa ne gwamnatin ta kafa dokar ta-baci.

A kasafin kudin kasar na bana, gwamnatin ta ware Naira biliyan biyu don sake gina yankin, to amma tuni wasu suka fara sukar gwamnatin suna cewa kudin sun yi kadan.

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ne ya ya yi alkawarin aiwatar da shirin tun lokacin da ya ziyarci yankin da rikicin Boko Haram ya shafa.

Minista a ma'aikatar harkokin kudin kasar Dr Yarima Ngama ya ce akwai kwamitocin da aka kafa da zasu zagaya jihohin da abin ya shafa, don tantance asara da barnar da aka yi kafin a fara fara aiwatar da shirin.