Pellegrini ne gwarzon koci a watan Disamba

Image caption Manuel Pellegrini

An baiwa kocin Manchester City Manuel Pellegrini kyautar gwarzon kocin gasar Premier ta Ingila na watan Disamba.

Manchester City wacce ke ta biyu a kan tebur, ta samu nasara a wasanni shida a watan da ya wuce sannan kuma ta buga canjaras a wasa guda.

Sannan kuma an baiwa dan kwallon Liverpool Luis Suarez, kyautar gwarzon dan kwallon premier na watan da ya gabata.

Suarez mai shekaru 26, ya zura kwallaye 10 a watan Disamba, ciki hadda kwallaye hudu da ya zura a ragar Norwich.

Karin bayani