Amurka ta tuhumi jami'ar jakandancin India

Jami'ar huldar diplomasiyyar India a Amurka Khobragade
Image caption Jami'ar huldar diplomasiyyar India a Amurka Khobragade

Amurka na tuhumar jami'ar huldar jakadancin India da laifin yin bizar karya da kuma bayar da bayanan karya.

An kama jami'ar, Devyani Khobragade ne a Amurka cikin watan Disamba kan zargin kin biyan mai aikinta albashin da ya dace.

Batun dai ya haifar da damuwa matuka a India, lokacin aka garkama wa jami'ar ankwa a hannu aka kuma lalube dukkan jikinta.

Yanzu haka dai an bukaci ta fice daga Amurkar bayan da India ta ki amincewa da bukatun Amurkar na cire mata rigar kariyar diplomasiyya.

Wannan takaddamar ta haifar da dage ziyarar sakataren harkokin makamashi na Amurka Earnest Moniz da aka shirya zuwa India.