Amurka ta aike sojoji Somalia

Image caption Amurka ta tura sojojin bada shawara zuwa Somaila

Amurka ta bayyana cewa ta aike da wasu sojoji masu bada shawara zuwa Somalia a 'yan watannin nan.

Wani mai magana da yawun rundunar sojojin Amurkan ta Afirka Kanal Tom Davis, ya ce masu bada shawarar suna zaune ne a filin jirgin sama na birnin Mogadishu, kuma suna taimakawa dakarun Somalia dana Tarayyar Afirka ne a yakin da suke yi da mayakan Al Shabab

Sojojin da aka tura dai basu kai su biyar ba, kuma sune na farko da aka aika Somaliar tun lokacin da dakarun Amurkar suka janye daga kasar shekaru 20 da suka gabata, jim-kadan bayan wasu sojoji goma sha takwas sun mutu a lokacin da aka kakkabo wani jirgin helicoptar Amurkar

A watan nuwamba ne dai kwamitin sulhun majalisar dinkin duniya ya amince ya fadada dakarun Afirka masu aikin kiyaye zaman lafiya a Somalia, inda a yanzu rundunar take da sojojin da suka haura 22,000.

Karin bayani