Djotodia ya yi gudun hijira zuwa Benin

Tsohon shugaban jamhuriyar tsakiyar Afrika, Michel Djotodia, ya tafi gudun hijira a jamhuriyar Benin.

Michel Djotodia wanda ya sauka a jiya, ya yi ta fuskantar matsin lamba daga kasashen duniya, kan yadda ya gaza kawo karshen rikicin addinin da kasar ta tsunduma.

Shi ne Musulmi na farko da ya zama shugaban kasar.

Rikici ya ci gaba a kasar, tsakanin bangarorin 'yan daba biyu masu gaba da juna a kasar, tun bayan saukarsa.

A Bangui, babban kasar, an wasashe shaguna da gidajen Musulmi.