'Al Sisi zai tsaya takarar shugaban ƙasa'

Kafafen yada labaran hukuma a Masar na bada rahotannin cewa, shugaban rundunar sojan kasar, Janar AbdulFattah Al-Sisi ya ce zai shiga takarar shugaban ƙasa.

Rahotannin na cewa Al-Sisi ya ce, idan dai jama'a suka nuna bukata zai tsaya takarar shugaban kasa.

Wannan dai na kara ƙarfafa raɗe-raɗin cewa, zai tsaya takarar shugaban kasar da za a gudanar nan gaba a bana.

Jaridar Al Ahram ta ambaci Janar Sisi yana cewa, zai kuma bukaci goyon bayan rundunar sojan kasar.

Masu aiko da rahotanni na cewa, Janar Sisi na kara samun goyon baya, sakamakon rawar da ya taka wajen tumbuke shugaba Muhamad Mursi mai ra'ayin Musulunci, a bara.