Isra'ila: Sharon ya mutu

Image caption Marigayi Sharon

Tsohon Praministan Isra'ila, Arial Sharon ya mutu, yana dan shekaru tamanin da biyar.

Ya kasance cikin dogon suma tun shekara ta 2006 bayan ya hadu cutar bugun jini.

Cikin 'yan kwanakin nan dia halin da yake ciki ya tsananta, yayin da wasu muhimman sassan jikinsa da suka hada koda da suka daina aiki.

Sharon dai ya taka rawa sosai a tarihin Isra'ila, a matsayin janar din soja, daga baya kuma ya fada fagen siyasa.

Sai dai kuma duk tsawon rayuwarsa mutum ne da ya kasance ana cece-kuce akansa.