Shin waye Margayi Ariel Sharon ?

Image caption Ariel Sharon

Ariel Sharon wanda aka yi wa lakabi da 'The Bulldozer' ya yi matukar fice a siyasar kasar, kuma 'yan Isra'ila na kallonsa a matsayin gwarzon yaki wanda ya taimaka a yakin da aka yi shekarar 1967 da kuma 1973.

Amma galibin Palasdinawa na kallonsa a matsayin mai kisan rashin imani wanda keda hannu wajen kashe dubban fararen hula a sansanonin Sabra da Shatila a Lebanon a shekarar 1982.

A karshen rayuwarsa, Sharon ya yi matsin lamba a kan ficewa daga zirin Gaza abinda 'yan jam'iyyarsu a Israila suke adawa dashi a kai.

Sharon an rada masa sunan Ariel Scheinerman lokacin haihuwarsa a yankin tuddan Sharon a shekarar 1928 dake Palasdinu a karkashin mulkin turawan Birtaniya.

Image caption Sharon a fagen yaki

Iyayensa Shmuel da Devorah manoma ne wadanda su ka yi kaura daga Rasha, kuma gonarsu ta kasance cikin fuskantar matsala daga makiyaya Larabawa abinda ya sa tun yana dan karami ya koyi fada.

'Gwarzon da aka raunata'

Tun yana dan karami, ya kan burne bindigogin iyayensa a cikin juji idan dakarun Birtaniya su ka kawo rangadi.

A makarantar sakandare a Tel Aviv ya karanci fannin aikin gona da siyasa da kuma harkokin tsaro.

Yana da shekaru 14, Sharon ya shiga cikin kungiyar Haganah, wato dakarun karkashin kasa na yahudawa kuma bayan shekaru shida wato a shekarar 1948, sai ya zama kwamandan lokacin da aka kafa Isra'ila.

A wani lokacin na taba harbinsa a ciki lokacin yaki kuma a duk motar da yake ciki, yana cika ta da barasa.

'Mukamin Siyasa'

Image caption Sharon ya dade yana jinya

A kokarinsa na samun mukamin siyasa, a shekarar 1972, Sharon ya fita daga cikin sojin Isra'ila inda ya kafa jam'iyyar Likud.

Amma kuma a watan Okotoban 1973 an bukaceshi ya koma soja saboda wasu hare-hare da Masar da kuma Syria su ka kai.

Da ya kara komawa siyasa, sai aka zabe Sharon a majalisar wakilan Isra'ila wato Knesset.

A tsakiyar shekarun 1970, ya kasance mashawarci ta fannin tsaro ga Firaministan wancan lokacin Yitzhak Rabin kafin ya zama ministan ayyukan gona a shekarar 1977.

Daga shekara ta 2001 kuma zuwa 2006 ya kasance Firaministan Isra'ila.

A watan Disambar 2005 ne kuma ya kamu da bugun zuciya kuma yake cikin rai-kwakwai-mutu-kwakwai na tsawon shekaru bakwai kafin ya mutu.

Karin bayani