An fara jana'izar Ariel Sharon

Marigayi tsohon Piraministan Isra'ila Ariel Sharon
Image caption Marigayi tsohon Piraministan Isra'ila Ariel Sharon

Nan bada jimawa bane za a ajiye akwatin gawar tsohon Piraministan Isra'ila Ariel Sharon da ya mutu a ranar asabar, don shirin jana'izarsa.

Wakiliyar BBC ta ce an dauke gawarsa daga asibiti kuma a yau Lahadi za a ajiye akwatin gawar a majalisar dokokin Isra'ila, saboda jama'a su sami damar yi masa ban kwana.

Za a binne shi a ranar Litinin a gonarsa ta Negev dake kudancin Isra'ila, ana kuma tsammanin shugabanni daga sassan duniya zasu halarci jana'izarsa ciki harda mataimakin Shugaban Amurka Joe Biden.

Ariel Sharon ya mutu yana da shekaru tamanin da biyar, ya kuma kasance cikin dogon suma tun a shekara ta 2006 bayan ya hadu da cutar bugun jini.