An ɗan samu sasantawa a birnin Bangui

Yayin da ake ci gaba da zaman ɗar-ɗar a jamhuriyar Afirka ta tsakiya, an ayyana sasantawa a wani ɓangare na Bangui babban birnin kasar.

Shaidu sun ce, mayakan sojan sa kai na musulmi, wato Seleka da kuma mayakan sojan sa kai na Krista, wato Anti Balaka sun nemi gafarar juna.

Masu aiko rahotanni sun ce, al'mura sun dan lafa a birnin Bangui, idan aka kwatanta da irin halin da aka shiga jiya Asabar.

Mutane sama da dubu daya ne aka kashe, a rikicin na addini, wanda ya barke bayan Mr Djotodia ya kwace iko a watan Maris na bara.

Nan da makonni biyu masu zuwa ake fatan nada sabon shugaban kasa na rikon kwarya.