An harbe mataimakin Ministan Masana'antun Libya

Jami'an Sojin kasar Libya
Image caption Jami'an Sojin kasar Libya

An harbe mataimakin ministan masana'antun Libya Hassan al-Drou'i a lokacin da ya kai ziyara garinsu na Sirt, dake gabashin birnin Tripoli.

Kafofin yada labaran yankin sun ambato jami'an tsaro na cewa an kashe mataimakin Ministan ne kusa da wata kasuwa dake tsakiyar bangaren garin.

Ba'a dai san, ko su waye suka kashe shin ba

Tunda farko dai Jami'ai a Libyan sunce an kashe akalla mutane goma sha biyar, aka kuma jikkata mutum ashirin, a wani artabun da aka yi tsakanin kabilu masu gaba da juna a kudancin Kasar.

Kisan wani mai tsaron lafiyar jagoran 'yan bindigar birnin Sabha ne dai ya tunzura rikicin, wanda kuma mamba ne na 'yan kabilar Awlad Soliman, kuma 'Yan wadannan kabilar ne suka zargi 'yan kabilar Tubu da kisan mutumin.

Rikicin dai shine mafi muni tsakanin kabilu tun lokacin da aka cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a watan Maris din shekarar 2012, bayan wani mummunan rikici daya haddasa mutuwar mutane fiye da 150.