Kabilun Yankin Tesker sun sasanta da junansu

Mahammadou Issoufou
Image caption Kabilun yankin Tesmer sun sha fama da rikici a baya

A jamhuriyar Nijar a ranar Asabar ne aka kawo karshen zaman taron sasanta juna tsakanin kabilun yankin Tasker.

Wakilan kabilun Tubawa da Larabawa da Bugaje da fulani sun tattauna matsalolin dake haddasa tashin hankalin tsakaninsu.

Batun satar dabbobi ne dai, ke- kan gaba a jerin abubuwan dake hadasa tashe-tashen hankulan.

Kabilun yankin sun ce sun zama 'tsintsiya daya madaurinki daya'.

Karin bayani