Peres ya jagoranci alhinin rasuwar Sharon

Shugaban Isra'ila, Shimon Peres ya jagoranci masu nuna alhani game da mutuwar tsohon praministan kasar, Ariel Sharon, a wajen majalisar dokokin kasar Knesset.

Mr Peres ya shimfida wasu furanni kana ya tsaya ƙyam, domin nuna girmamawa, kafin sauran jama'a su bi bayansa.

Palasɗianwan ƙauyen Qibya na sun ce, suna tuna Sharon ne a matsayin mai yin kisan rashin imani.

A jiya ne Sharon ya mutu bayan ya kwashe shekaru takwas cikin wani yanayi na dogon suma.

A gobe Litinin 'yan siyasa zasu yi wani zama na musamman na tunawa da Sharon kafin a binne shi.