'Yan tawayen Sudan ta Kudu sun ce an gana da jagoransu

Riek Machar, jagoran 'yan tawaye
Image caption Riek Machar, jagoran 'yan tawaye

Wata sanarwa daga 'yan tawayen Sudan ta Kudu na cewa wakilin Amurka, Donald Booth, da kuma wakilan kasashen yankin masu shiga tsakani, sun tattauna da jagoran 'yan tawayen Riek Machar, a wani wurin da ba a bayyana ba , a cikin kasar Sudan ta Kudun.

Takardar sanarwar wadda kampanin dillacin labarun Faransa ya samu, ta ce an yi ganawar ce a jiya, Asabar.

Babu wata majiya mai zaman kanta da ta tabbatar da hakan.

Ba a samu wani ci gaban a zo a gani ba, a tattaunawar sulhun da aka yi a Ethiopia da nufin kawo karshen makonni hudun da aka kwashe ana tashin hankali, kuma babban abin da ake ganin ya zame kadangaren bakin tulu, shi ne bukatar da Mr Machar ya gabatar na sai a sako wasu magoya bayansa su goma sha daya da ake tsare da su.