Ana cin naman mutane a rikicin CAR

Image caption "Mahaukacin kare" mai cin naman Musulmi danye.

Yayin da ake ci gaba da samun zaman zulumi tsakanin mayakan sa-kai na Kirista da Musulmi a Jamhuriyyar Afirka ta tsakiya, BBC ta gano wani mummunan nau'in rikicin mai tsoratarwa a baya bayan nan, a babban birnin Kasar na Bangui.

Wani ganau ya shaidawa BBC wani al'amari, inda wani mutum da aka fi sani da suna Mad Dog wato 'Mahaukacin kare' ya sare kafar wani Musulmi, sannan yaci naman kafar Musulmin danye.

Musulmin ya mutu ne a cikin wani mummunan turmutsutsu.

Mutumin da ya aikata wannan aiki mai tsoratarwa ya fadawa BBC cewa ya yi hakan ne a matsayin ramuwar gayya, bayan da ya ce Musulmi sun kashe masa matarsa mai juna biyu, da 'yar uwarsa da kuma jaririnta.

Karin bayani