'Zaman kara zube ya zo karshe'

Wasu mazauna Bangui
Image caption Wasu mazauna Bangui suna murnar kawo karshen fada a Bangui

Shugaban riko na Jamhuriyar tsakiyar Afruka, kasar da ke fama da mummunan tashin hankali, ya bayyana cewar lokacin zaman kara zube a kasar ya zo karshe.

A lokacin da yake jawabi a hedkwatar 'yan sanda da ke Bangui, babban birnin kasar, Alexandre-Ferdinand Nguendet, ya ce yana yin gargadi mai tsanani ga sojojin sa kai da masu kwasar ganima, cewa, lokacin cin karensu babu babbaka ya kare.

Wakilin BBC a Bangui ya ce yanzu kura ta dan lafa a birnin, amma ya ce har yanzu dokar hana fitar dare tana aiki, kuma baa san bangaren dake iko ba.

Daruruwan sojojin da suka gudu daga rundunar sojojin kasar a can baya, yanzu suna komawa bakin aiki, sannan su ma 'yan sanda sun fara sintiri a kan titina.

Kungiyar agaji ta Red Cross ko Croix Rouge ta ce ta gaano wasu gawaki hudu a ranar Litinin bayan waniu tashin hankali da aka yi a cikin daren Lahadi.

Karin bayani